Ba a taba cire Ramos a zagaye na biyu a Champions ba tun 2015

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Real Madrid za ta karbi bakuncin Atalanta wasa na biyu a zagayen zuwa Quarter finals ranar Talata a Alfredo Di Stefano.

Cikin wadanda za su buga wa Real wasa har da kyaftin, Sergio Ramos, wanda ya yi jinyar kwana 58 da rashin buga karawa 10.

Real ce ta yi nasara a wasan farko da suka fafata a Italiya da ci 1-0 ranar 24 ga watan Fabrairu, kuma Ferland Mendy ne ya ci mata kwallon.

Abu ne mai mahimmaci da Ramos zai yi wa Real karawar, saboda mahimmaci ga kungiyar da kuma kwarewar da yake da ita a gasar ta Zakarun Turai.

Kyaftin din zai bayar da gudunmuwa a Real, musamman gurbin tsaron baya, sakamakon dan wasan Brazil, Casemiro ba zai buga karawar ba, sakamakon karbar katin gargadi a Italiya.

Ramos mai shekara 34 bai taba yin rashin nasara a zagaye na biyu tare da Real Madrid ba a Champions League tun mayun 2015 da Juventus ta fitar da kungiyar Spaniyar.

A kaka biyu da ta wuce Ramos bai buga wasan da Ajax ta fitar da Real ba da wanda Manchester City ta kai zagayen Quater finals, bayan cin Madrid.

Real Madrid ta buga karawar zagaye na biyu a Champions League tare da Ramos sau 63, inda ta ci wasa 33 da canjaras 10 aka doke ta 20 daga ciki.

Real tana ta uku a teburin La Liga na bana da maki 57 da tazarar maki biyu tsakaninta da Barcelona ta biyu, bayan da Atletico ce ta daya mai maki 63.

Tuni kuma kocin Real, Zinedine Zidane ya bayyana 'yan wasa 19 da za su fuskanci Atalanta a ranar ta Talata.

'Yan wasan Real Madrid su 19:

Masu tsaron raga: Courtois da Lunin da kuma Altube.

Masu tsaron baya: E. Militao da Sergio Ramos da R. Varane da Nacho da Marcelo da kuma F. Mendy.

Masu buga tsakiya: Kroos da Modric da Valverde da kuma Isco.

Masu cin kwallaye: Benzema da Asensio da Lucas V. da Vini Jr. da Rodrygo da kuma Hugo Duro.