Man City ta daura damarar lashe kofi hudu a bana

Pep Guardiola

Asalin hoton, Getty Images

Manchester City ta kai zagayen Quarter finals a Champions League karo na hudu a jere, bayan da ta doke Borussia Monchengladbach 4-0 gida da waje ranar Talata.

City ta ci kwallon farko ta hannun Kevin de Bruyne, sannan Illkay Gundogan ya kara na biyu a fafatawar da suka yi a Bucarest.

Kungiyar ta Etihad ta ci 2-0 a wasan farko da shima suka barje gumi a Puskas Arena cikin Fabrairu, sakamakon dokar hana zirga-zirga tsakanin Jamus da Burtaniya don gudun yada cutar korona.

Ranar Juma'a za a yi bikin raba jadawalin zagayen daf da na kusa da na karshe a gasar ta zakarun Turai.

Da wannan sakamakon na nufin City ta yi rashin nasara a wasa daya daga 32 da ta fafata da hakan ke haska za ta iya lashe kofi hudu a kakar bana.

Kofin da kungiyar ke hari sune Premier League da Champions League da FA Cup da kuma Caraboa Cup.

Kawo yanzzu City wadda take ta daya da tazarar maki 14 a Premier League ta kai Quarter finals a FA Cup da karawar karshe a Caraboa Cup da wasan daf da na kusa da na karshe a Champions League a bana.

A bara City ta kawo wannan matakin Quarter finals ne, bayan da ta yi nasara a kan Real Madrid a gasar ta Champions League.