Pogba ya kai Man United Quarter finals a Europa na bana

Europa League

Asalin hoton, Getty Images

Paul Pogba ya kai Manchester United wasan daf da na kusa da na karshe a Euopa League, bayan da ya ci Milan kwallo daya a San Siro ranar Alhamis.

Dan wasan tawagar Faransa ya yi wannan bajintar a mintu uku da aka sa shi wasa a zagaye na biyu a karawar. Wasan farko da suka yi a Old Trafford tashi suka yi 1-1.

Wannan ne wasan farko da dan kwallon mai shekara 28 ya buga wa kungiyar tamaula, bayan jinya a raunin da ya yi tun 6 ga watan Fabrairu.

Kafin kwallon da Pogba ya ci, United ta fuskanci kalubale da dama a hannun Milan din, wadda ta yi ta kokarin cin kwallo a wasan.

Tun kan hutu 'yan wasan Milan sun kai hare-hare da suka hada da Rade Krunic da Alexis Saelemaekers da kuma Theo Hernandez, amma ba su samu damar cin kwallo ba,

Milan ta saka Zlatan Ibrahimoch a fafatawar ko zai samar mata abin da take bukata, kuma kadan ya rage ya ci kwallo, amma golan United, Dean Henderson ya hana su ji kunya a Italiya

United ta kai wasan daf da na kusa da na karshe tare da Arsenal, kuma ranar Juma'a za a raba jadawalin Quarter finals da na daf da karshe.