Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Haaland, Moriba, Mbappe, Aguero, Pogba

Erling Braut Haland

Asalin hoton, Getty Images

Real Madrid da Barcelona sun shirya gogayya da Manchester City, Manchester United da kuma Chelsea a yunkurin daukar dan wasan Borussia Dortmund da Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 20. (AS - in Spanish)

Haaland yana son barin Dortmund a bazarar nan kuma ya matsu ya tafi Real Madrid. (ABC - in Spanish)

Manchester United na sha'awar daukar dan wasann Barcelona dan asalin kasar Guniea da ke buga gasar 'yan kasa da shekara 17 a Sifaniya Ilaix Moriba, mai shekara 18. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Paris St-Germain ta shirya sabunta kwangilar dan wasan Faransar Kylian Mbappe, mai shekara 22, inda za ta ba shi euro 30m (£25.8m) domin hana Real Madrid da Liverpool daukarsa. (L'Equipe via Mirror)

Barcelona na son daukar dan wasan Manchester City da Argentina Sergio Aguero, mai shekara 32, da kuma dan kwallon Liverpool dan kasar Netherlands Georginio Wijnaldum, mai shekara 30, a lokacin musayar 'yan kwallo na bazara. (AS via Sport Witness)

Juventus na ci gaba da sanya ido kan halin da dan wasan Manchester United Paul Pogba yake ciki, a yayin da kwangilar dan wasan na Faransa mai shekara 28 za ta kare a watan Yunin 2022. (Calciomercato - in Italian)

Tottenham za ta yi asarar £25m idan ta sallami kocinta Jose Mourinho daga aiki. (Mirror)

Barcelona za ta bai wa dan wasan Argentina Lionel Messi, mai shekara 33, kwangila ta tsawon rayuwarsa a bazarar nan a yunkurin da take yi na hana shi barin kungiyar amma za ta nemi ya amince a rage albashinsa. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Har yanzu West Ham ba ta tattauna game da sayen dan wasan Manchester United da Ingila Jesse Lingard, baki daya ba. Dan wasan mai 28 yana zaman aro a kungiyar. (Football London)

Napoli na sha'awar dan wasan Liverpool dan kasar Girka Kostas Tsimikas, mai shekara 24, wanda sau shida kawai ya murza leda tun da ya je kungiyar a bazarar da ta wuce. (Corriere dello Sport via Sport Witness)

Liverpool da Tottenham sun bayyana sha'awarsu ta daukar dan wasan Amurka Matthew Hoppe, mai shekara 20, daga Schalke. (Transfermarkt - in German)

Ana duba yiwuwar nada tsohon kocin Juventus Massimiliano Allegri a matsayin kocin Napoli domin ya maye gurbin Gennaro Gattuso. (Calciomercato - in Italian)