Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Suarez, Torres, Costa, Kane, Ronaldo da Johnstone

Luiz Suarez

Asalin hoton, Getty Images

Liverpool na sha'awar sake daukar dan wasan Atletico Madrid dan kasar Uruguay Luis Suarez, mai shekara 34. (Fichajes via Four Four Two)

Dan wasan Atletico Madrid dan kasar Sifaniya Diego Costa, mai shekara 32, zai koma murza leda a Benfica a kakar wasa mai zuwa bayan ya cimma yarjejeniya da kungiyar ta Portugal. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Tsohon shugaban Real Madrid Ramon Calderon ya ce kungiyar ba ta da kudin sayen dan wasan Tottenham da Ingila Harry Kane, mai shekara 27, a bazarar nan. (Talksport)

Real na son dawo da dan wasan Sifaniya Brahim Diaz, mai shekara 21, bayan ya tafi zaman aro a AC Milan. (Calciomercato - in Italian)

Sai dai kungiyar ba ta son komowar dan wasan Juventus dan kasar Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 36. (COPE - in Spanish)

Dan wasanVillarrealdan kasar Sifaniya mai shekara 24 Pau Torres zai so tafiya Manchester United a bazarar nan. (Manchester Evening News)

Tsohon dan wasan Tottenham Alan Hutton ya nemi kungiyar ta dauki golan Ingila Sam Johnstone dagaWest Brom domin maye gurbin Hugo Lloris. (Football Insider)

Tsohon dan wasan Arsenal Ian Wright ya ce ya kamata Arsenal ta dauki dan kasar Norway Martin Odegaard, mai shekara 22, a matsayi na dindindin dagaReal Madrid a bazarar nan. (Ringer FC's Wrighty's House podcast via Metro)

Sunderland ta soma tattaunawa da Wolves domin sayen dan wasan Ingila da ke zaman aro Dion Sanderson, mai shekara 21, a kan £2m. (Daily Mail)

Dan wasan gaba na Faransa Antoine Griezmann, mai shekara 30, yana son zama a Barcelonadomin ya nuna irin kwazonsa. (Radio Catalunya via AS)

Barcelona na son sayar da Griezmann da kuma dan wasan tsakiya na Brazil Philippe Coutinho, mai shekara 28. (El Confidencial - in Spanish)

Dan wasan Chelsea Christian Pulisic, mai shekara 22, ya ce yana son wakiltar Amurka a gasar Olympic da za a yi a Tokyo. (NBC Sports via Evening Standard)