Real ta maimaita cin Liverpool irin na kaka biyu da ta wuce

Real Madrid vs Liverpool

Asalin hoton, Real Madrid

Liverpool ta yi rashin nasara da ci 3-1 a hannun Real Madrid a wasan farko karawar daf da na kusa da na karshe da suka fafata a Spaniya.

Real ta fara cin kwallo ta hannun Vinicius Junior a minti na 27 da fara wasa, sannan ta kara na biyu ta hannun Marco Asensio.

Bayan da suka yi hutu suka koma karawa ta biyu ne Liverpool ta zare kwallo daya ta hannu Mohamed Salah.

Real Madrid ta kara sa kwazon da ya kai ta cin kwallo na uku ta hannun Vinicius Junior kuma na biyu da ya zura a raga a wasan na ranar Talata.

Irin wannan sakamakon Real ta ci Liverpool ranar 26 ga watan Mayun 2018 a Kiev a wasan karshe da ta lashe Champions League kuma na 13 jumulla.

Real ta buga wasan ne ba tare da kyaftin dinta Sergio Ramos wanda ke jinya da kuma Raphael Varane wanda ya kamu da cutar korona a makon jiya.

Liverpool za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasa na biyu na quarter finals ranar 14 ga watan Afirilu.

Kungiyoyin biyu sun lashe kofin Champions League 19 a tsakaninsu, inda Real Madrid take da 13, ita kuwa Liverpool ta dauki guda shida.

'Yan wasan da kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya fuskanci Liverpool a wasan quarter finals a Champions League ranar Talata.

'Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Courtois da Lunin da kuma Altube.

Masu tsaron baya: E. Militao da Nacho da Marcelo da Odriozola da kuma F. Mendy.

Masu buga tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Valverde da Isco da kuma Arribas.

Masu buga gaba: Benzema da Asensio da Lucas V. da Vini Jr. da Mariano da kuma Rodrygo.