An dakatar da Neymar daga buga wasa biyu a Ligue 1

PSG

Asalin hoton, Getty Images

An dakatar da dan wasan Paris St Germain, Neymar daga buga gasar Ligue 1 biyu, sakamakon jan kati da aka yi masa ranar Asabar a karawa da Lille.

A ranar Laraba kwamitin da'a na hukumar buga kwararriyar gasar Faransa ya sanar da wannan hukuncin.

An kori Neymar daga karawar, bayan da ya ture Tiago Djalo, wanda shima ya aikata ba dai-dai ba a wasan da ta kai aka koreshi a fafatawar.

Tun farko an dakatar da Neymar wasa uku ne daga baya aka ce sun koma biyu, inda ba zai buga karawa da Strasbourg ranar Asabar ba da na St Etienne a makon gaba.

Haka shima Djalo an dakatar da shi buga wasa biyu, amma an mayar da shi karawa daya ce ba zai buga ba.

Neymar wanda ya buga Ligue 1 a karshen makon a karon farko tun bayan jinyar wata biyu, ya karbi jan kati sau uku a karawa 15 da ya yi a gasar ta Faransa.

Lille ce ta yi nasara a wasan da ci 1-0 ta kuma ci gaba da zama ta daya a kan teburi da tazarar maki uku tsakaninta da Paris St Germain.