PSG ta fitar da Bayern mai rike da Champions League

Asalin hoton, Getty Images
Paris St Germain ta kai wasan daf da karshe duk da rashin nasara da ta yi a hannun Bayern Munich da ci 1-0 a Champions League ranar Talata.
Tsohon dan wasan PSG, Eric Maxim Choupo-Moting ne ya ci wa Bayen kwallon saura minti biyar su je hutu.
PSG ta kai matakin gaba ne, bayan da ta yi nasara da ci 3-2 a wasan farko da suka buga a Jamus ranar Laraba, kenan sun tashi 3-3 gida da waje kenan.
Kwallaye ukun da kungiyar ta Faransa ta zura a raga a Jamus, sune suka kai ta wasan daf da karshe a gasar bana ta cin kofin zakarun Turai.
Kungiyoyin biyu sun kara a bara a wasan karshe, inda Bayern ta yi nasara da ci 1-0 ta kuma lashe Champions League na shida jumulla.
Kungiyar Faransa za ta fuskanci wadda ta yi nasarar kai wa daf da karshe tsakanin Borussia Dortmund ko Manchester City da za su fafata ranar Laraba.
A wasan farko da suka buga a makon jiya, City ce ta yi nasara da ci 2-1.
'Yan wasan PSG da ke taka leda a Bayern:
Coman da Choupo-Moting da kuma Tanguy Nianzou.
'Yan kwallon Bayern da ke PSG:
Draxler da Diallo da Thilo Kehrer da kuma Bernat.
'Yan wasan Paris St Germain da suka fuskanci Bayern:
- Keylor Navas
- Sergio Rico
- Yanis Saidani
- Mitchel Bakker
- Abdou Diallo
- Timothée Pembélé
- Presnel Kimpembe
- Alessandro Florenzi
- Colin Dagba
- Thilo Kehrer
- Rafinha
- Ander Herrera
- Idrissa Gueye
- Danilo Pereira
- Abdoulaye Kamara
- Leandro Paredes
- Marco Verratti
- Pablo Sarabia
- Neymar JR
- Julian Draxler
- Angel Di Maria
- Kylian Mbappé
- Moise Kean
- Kenny Nagera






