Man United ta kai daf da karshe a Europa League

Manchester United

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United ta kai zagayen daf da karshe a gasar Zakarun Turai ta Europa League ta bana.

United ta yi nasara cin Granada 2-0 a wasa na biyu da suka fafata a Old Trafford zagayen quarter finals ranar Alhamis.

Minti shida ta take leda Edinson Cavani ya ci wa United kwallo, sannan daf da za a tashi daga karawar Jesus Vallejo ya ci gida.

A wasan farko da suka buga a makon jiya, United ce ta ci 2-0 a Spaniya, hakan na nufin ta kai daf da karshe da cin kwallo 4-0 gida da waje kenan.

United za ta karbi bakuncin Roma a wasan farko na daf da karshe ranar Alhamis 29 da watan Afirilu, sannan su buga karawa ta biyu ranar 6 ga watan Mayu a Roma.

Roma ta kai daf da karshe a gasar ta Europa League, bayan da ta yi nasara da ci Ajax 3-2 gida da waje.

United tana ta biyu a teburin Premier League da tazarar maki 11 tsakaninta da Manchester City mai jan ragamar teburin bana.

Ranar Lahadi 18 ga watan Afirilu, Manchester United za ta karbi bakuncin Burnley a gasar Premier League ranar Lahadi a Old Trafford.

Burnley tana ta 16 a kasan teburin wasannin bana da maki 33, bayan wasa 31 da ta buga.