City ta fita daga European Super League Chelsea za ta bi baya

European Super League

Asalin hoton, Getty Images

Manchester City ta fita daga sabuwar gasar European Super League, ita ma Chelsea za ta yi hakan.

Wannan matakin ya zo ne kwana daya da aka sanar cewar Chelsea da City suna daga cikin kungiyoyi shida daga Premier League da suka amince su gudanar da sabuwar gasar.

A ranar Lahadi aka sanar da kungiyoyi 12 da ke shirin fara sabuwar gasar zakarun Turai, sai dai an yi ta caccakar wannan sabon yunkurin.

Sama da magoya bayan Chelsea 1,000 suka taru a Stamford Bridge kafin wasan da za ta kara da Brighton a Premier, inda suka nuna bacin rai da kungiyar ta fada wannan shirin.

Chelsea da Manchester City suna daga cikin kungiyoyin Ingila shida da suka amince su shiga sabuwar gasar har da Arsenal da Liverpool da Manchester United da kuma Tottenham.

Kungiyoyi 12 ne suka sanar a ranar Lahadi cewar za su gudanar da gasar zakarun Turai ta European Super League da za su dunga fafatawa tsakiyar mako.

Hukumomin kwallon kafa da gwamnatin Burtaniya sun yi watsi da wannan shirin, har da hukumar kwallon kafa ta Turai da ta duniya, Fifa.

Chelsea ce ta fara ayyana cewar za ta fice daga sabuwar gasar da ake son gudanarwa.

Kungiyar Stamford Bridge da ta Ettihad ba sune kashin bayan wannan shirin ba, kuma sune na karshe da aka sa a cikin tsarin.