An naɗa Jose Mourinho a matsayin kocin Roma

Asalin hoton, Getty Images
Roma ta sanar da naɗa Jose Mourinho a matsayin kocinta a kaka mai zuwa
Mournho mai shekara 58 ya maye gurbin Paulo Fonseca wanda Roma a ranar Talata ce zai bar ƙungiyar idan an kammala kaka.
A ranar 19 ga watan Afrilu Tottenham ta kori Mourinho. Yanzu ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara uku a Roma.
"Ƙaunar magoya bayan Roma ya sa na amince da akin kuma na matsu a fara kaka mai zuwa," in ji Mournho.
An kori Mourinho ne baan watanni 17 yana horar da Tottenham bayan abubuwa sun taɓarɓarewa ƙungiyar a tsakiyar kaka inda ta rikito zuwa tsakiyar tebur.
A bana sau 10 ana doke Mournho kuma karon farko a tarihinsa na horar da ƴan wasa.
Mournho ya taɓa horar da Inter Milan inda ya lashe kofuna huɗu a kaka biyu.
A kaka ɗaya ta lashe wa Inter kofuna uku da ya ƙunshi har da kofin zakarun Turai da Seria da kuma Coppa Italia.






