'Yan Real Madrid da suka sha kashi a Stamford Bridge

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Real Madrid ta yi rashin naasara a hannun Chelsea da ci 2-0 a wasa na biyu na daf da karshe a Champions League da za su fafata a Stamford Bridge.

A makon jiya ranar Talata kungiyoyin suka tashi 1-1 a Spaniya a wasan farko na daf da karshe a gasar ta Zakarun Turai.

Chelsea ta kai wasan karshe da ci 3-1 kenan gida da waje, za kuma ta kara da Manchester City a ranar 29 ga watan Mayu a Istanbul.

Wannan shi ne karo na biyu da kungiyoyin Ingila za su buga wasan karshe a Champions League, bayan wanda Liverpool ta doke Tottenham a 2019.

Yanzu dai kofin La Liga ya rage a gaban Real Madrid idan ba haka ba za ta kare kakar bana ba tare da kofi ba.

Real din tana mataki na biyu a kan teburin La Liga da maki 74, irin wanda Barcelona keda shi mai mataki na uku.

Atletico Madrid ce ke matakin farko da maki 76, kuma saura karawa hurhudu a karkare kakar bana ta La Liga, wanda Real ke rike da kofin.

'Yan wasan Real Madrid da suka je Ingila karawa da Chelsea:

Masu tsaron raga: Courtois da Lunin da kuma Altube.

Masu tsaron baya: E. Militao da Sergio Ramos da Nacho da Marcelo da Odriozola da Mendy da kuma Miguel.

Masu buga tsakiya: Kroos, Modric da Casemiro da Isco da Valverde da Arribas da kuma Blanco.

Masu cin kwallaye: Hazard da Benzema da Asensio da Vini Jr. da Mariano da kuma Rodrygo.

Wasannin mako na 35 da za a buga a La Liga:

Ranar Juma'a 7 ga watan Mayu

  • Real Sociedad da Elche

Ranar Asabar 8 ga watan Mayu

  • Deportivo Alaves da Levante
  • Barcelona da Atletico Madrid
  • Cadiz da Huesca
  • Athletic Bilbao da Osasuna

Ranar Lahadi 9 ga watan Mayu

  • Getafe da Eibar
  • Valencia da Real Valladolid
  • Villarreal da Celta de Vigo
  • Real Madrid da Sevilla

Ranar Litinin 10 ga watan Mayu

  • Real Betis da Granada