Tuchel ya kai Chelsea wasan karshe a Champions League

Thomas Tuchel

Asalin hoton, Getty Images

Chelsea ta kai wasan karshe a Champions League na bana, bayan da ta doke Real Madrid da ci 2-0 a wasan da suka buga a Stamford Bridge ranar Laraba.

Timo Werner ne ya fara ci wa Chelsea Kwallon farko a minti na 18 da fara tamaula, kuma haka suka je hutu kungiyar Ingila tana da ci daya a raga.

Saura minti biyar a tashi daga karawar kungiyar ta Stamford Bridge ta kara na biyu ta hannun Mason Mount da hakan ya tabbatar mata da kai wa wasan karshe a gasar bana.

A wasan farko na daf da karshe a gasar ta Champions League da suka yi ranar Talata a Spaniya sun tashhi 1-1.

Saboda haka Chelsea ta kai zagayen gaba da cin kwallaye 3-1 kenan.

Da wannan sakamakon Chelsea za ta buga wasan karshe da Manchester City ranar 29 ga watan Mayu.

Wasan da za su kara a Instanbul shi ne na uku da Chelsea ta kai karawar karshe a Champions League, bayan wanda Manchester United ta doke ta a 2008.

Wasa na biyu da Chelsea ta kai wasan karshe ta lashe Champions League shi ne a 2012 wanda ta doke Bayern Munich.

Ranar Talata Manchester City ta kai wasan karshe a karon farko a Champions League, bayan da ta doke Paris St Germain da ci 2-0 a wasan na biyu da 2-1 a karawar farko a Spaniya.

Wannan ne karo na biyu da kungiyoyin Ingila za su buga wasan karshe a Champions League cikin kaka uku, bayan da Liverpool ta ci Tottenham 2-0 a 2019.

Watakila a gasar Europa League a kakar bana a buga wasan karshe tsakanin kungiyoyin Ingila biyu wato Arsenal da Manchester United.

Ranar Alhamis Arsenal wadda ta yi rashin nasara a wasan farko a Spaniya da ci 2-1 a hannun Villareal za ta karbi bakuncin fafatawa ta biyu a Emirates.

Manchester United kuwa wadda ta sharara 6-2 a ragar Roma, za su fafata a wasa na biyu na daf da karshe a Italiya ranar Alhamis.

A cikin watan Janairu Chelsea ta nada Thomas Tuchel koci, wanda ya maye gurbin Frank Lampard a lokacin da kungiyar ba ta kokari a wasanninta.

Tuchel wanda yanzu Chelsea ke mataki na hudu a teburin Premier League, ya kai kungiyar wasan karshe a FA Cup da zai fafata da Leicester City ranar 15 ga watan Mayu.