Arsenal ta fada tsaka mai wuya kan zuwa gasar Turai ta badi

Mikel Arteta

Asalin hoton, Getty Images

Arsenal ta yi ban kwana da gasar Europa League ta bana, bayan da ta tashi 0-0 da Villareal a Emirates ranar Alhamis.

A wasan farko da suka fafata a makon jiya a Spaniya a wasan daf da karshe, Villareal ce ta yi nasara da ci 2-1, kungiyar Spaniya ta kai zagayen gaba da kwallo 2-1 kenan gida da waje.

Arsenal wadda ta sa ran kai wa wasan karshe don lashe Europa League na bana ta shiga tsaka mai wuya ganin tana mataki na tara a kan teburin Premier League na bana.

Arsenal wadda ta yi shekara 20 tana zuwa Champions League a jere ta koma buga Europa League, wanda sai ta yi da gasr ta samu shiga gasar badi.

Arsenal ta kai karawar karshe a Europa League a 2019 karkashin kocin Villareal, Unai Emery, amma ta yi rashin nasara da ci 4-1 a hannun Chelsea.

Wannan karon kuma tsohon kocin Arsenal, Unai Emery ne ya yi waje da Gunners a Europa League na bana.

Cikin watan Nuwambar 2019 aka sallami Emery daga jan ragamar Arsenal, bayan wata 18 yana jan ragamar kungiyar, inda Mikel Arteta ya maye gurbinsa.

Wasannin Premier League da suka gaban Arsenal:

Premier League Lahadi 9 ga watan Mayu

  • Arsenal da West Brom

Premier League Laraba 12 ga watan Mayu

  • Chelsea da Arsenal

Premier League Laraba 19 ga watan Mayu

  • Crystal Palace da Arsenal

Premier League Lahadi 23 ga watan Mayu

  • Arsenal da Brighton