Manchester United ta kai wasan karshe a Europa League

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United za ta buga wasan karshe da Villareal a gasar Europa League ta bana a karon farko karkashin Ole Gunnar Solskjaer.
United ta kai wannan matakin ne duk da rashin nasara da ta yi da ci 3-2 a gidan Roma da suka fafata ranar Alhamis.
A makon jiya United ta doke Roma da ci 6-2 a wasan farko na daf da karshe da suka yi a Old Trafford, kenan United ta ci 8-5 gida da waje kenan.
Edinson Cavani ne ya fara ci wa United kwallo, saura minti shida su je hutu, kuma haka karkare zagayen farko United ta ci kwallo daya.
Edin Dzeko ne ya farke wa Roma, sanan Bryan Cristante ya ci na biyu, minti takwas tsakanin United ta farke ta hannun Edison Cavani.
Daf da za su tashi daga karawar Roma ta ci kwallo na uku, bayan da Alex Telles ya ci gida, amma duk da haka kungiyar Roma ta yi waje daga Europa League na bana.
Rabon da United ta lashe kofi tun 2017 karkashin Jose Mourinho da ya ci Europa League.
United ta taba yin kaka biyar ba tare da cin kofi ba tsakanin 1985 zuwa 1990 daga baya ta lashe FA Cup, wanda daga shi ne Sir Alex Ferguson ya fara yin bajinta a kungiyar.
Mourinho wanda shi ne kocin da zai ja ragamar Roma daga farkon kakar badi kan yarjejeniyar shekara uku, bayan da sama da mako biyu Tottenham ta sallame shi daga aiki.






