Real Madrid ta ci gaba da zama ta biyu a La Liga

Nacho Fernandez

Asalin hoton, Getty Images

Real Madrid ta je ta yi nasara a kan Athletico Bilbao da ci 1-0 a wasan mako na 37 a gasar La Liga da suka kece raini ranar Lahadi a San Mames.

Real Madrid ta ci kwallon ta hannun Nacho Fernandez a minti na 23 da suka koma zagaye na biyu na karawar bayan hutu da suka yi.

Wannan shi ne wasa na uku da suka kece raini a tsakaninsu a bana, bayan da suka fara karawa a La Liga cikin watan Disamba, inda Real ta yi nasara da ci 3-1.

Sun kara a wasa na biyu a Spanish Super Cup ranar 14 ga watan Janairu, inda Athletic ta fitar da Real da ci 2-1.

Da wannan sakamakon Real ta ci gaba da zama a mataki na biyu a kan teburin La Liga da maki 81, yayin da Atletico ce ta daya mai maki 83

Barcelona ce ta uku mai maki 76, sai Sevilla ta hudu mai maki 74 a teburin gasar Spaniya ta bana.

'Yan kwallon Real Madrid da suka kara da Athletic Bilbao:

Masu tsaron raga: Courtois da Lunin da kuma Altube.

Masu tsaron baya: E. Militao da Nacho da Marcelo da Odriozola da kuma Miguel.

Masu buga tsakiya: Modric da Casemiro da Valverde da Isco da kuma Blanco.

Masu cin kwallo: Hazard da Benzema da Asensio da Vini Jr da Mariano da kuma Rodrygo.

Sakamakon karawar mako na 37 a gasar La Liga ranar Lahadi:

  • Deportivo Alaves 4-2 Granada
  • Athletic Bilbao 0-1 Real Madrid
  • Atletico Madrid 2-1 Osasuna
  • Barcelona 1-2 Celta Vigo
  • Real Betis 1-0 Huesca
  • Real Sociedad 4-1 Real Valladolid
  • Valencia 4-1 Eibar
  • Villarreal 4-0 Sevilla
  • Getafe 2-1 Levante
  • Cadiz 1-3 Elche

Wasannin mako na 38 da za a buga a gasar La Liga ranar 23 ga watan Mayu:

  • Celta Vigo da Real Betis
  • Osasunada Real Sociedad
  • Real Madrid da Villarreal
  • Sevilla da Deportivo Alaves
  • Real Valladolid da Atletico Madrid
  • Eibar da Barcelona
  • Elche da Athletic Bilbao
  • Levante da Cadiz
  • Granada da Getafe
  • Huesca da Valencia

Wadan da ke kan gaba a cin kwallaye a La Liga ta bana:

  • Lionel MessiBarcelona30
  • Gerard MorenoVillarreal 23
  • Karim BenzemaReal Madrid CF22
  • Luis SuarezAtletico Madrid20
  • Youseff En-Nesyri Sevilla 18
  • Alexander IsakReal Sociedad16
  • Jose Luis MoralesLevante 14
  • Iago AspasCelta de Vigo13
  • Rafa Mir Huesca 13
  • Kike GarciaEibar 12
  • Marcos LlorenteAtletico Madrid12
  • Antoine Griezmann Barcelona12
  • Santi MinaCelta Vigo12