Fulham ta jika wa Manchester United aiki

Ole Gunnar Solskjaer

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United da Fulham sun tashi 1-1 a wasan mako na 37 a gasar Premier League da suka kara ranar Talata a Old Trafford.

United ta ci kwallon ne ta hannun Edison Cavani a minti na 15 da fara tamaula, kuma haka suka je hutu kungiyar Old Trafford da kwallo daya a raga.

Sai dai Fulham wadda tuni ta fadi daga gasar Premier za ta koma buga Championship a badi ta farke ne ta hannun Joe Bryan sauran minti 14 a tashi daga wasan.

A wasan farko a kakar bana da suka kara a gidan Fulham a cikin watan Janairu, United ce ta yi nasara da ci 2-1.

Da wannan sakamakon United wadda ta buga wasa 37 a gasar Premier tana da maki 71 a matakinta na biyu.

Hakan na nufin ba tabbas idan za ta karkare a matsayi na biyu a gasar bana, sai dai idan Leicester ta yi rashin nasara a hannun Chelsea ranar Laraba.

Leicester wadda za ta ziyarci Chelsea tana mataki na uku da maki 66, ita kuwa kungiyar Stamford Bridge tana ta hudu da tazarar maki biyu tsakaninta da kungiyar King Power.

United ta kasa hada maki tara a jere a Old Trafford da ya kamata ta samu a Premier, bayan da Leicester City ta doke ta 2-1 ranar 11 ga watan Mayu.

Kwana biyu tsakani Liverpool ta yi nasara a kan United a gida da ci 4-2, inda ta bai wa kungiyar Anfield damar fatan karkare kakar bana cikin 'yan hudun farko.

United za ta ziyarci Wolverhampton Wonderers ranar 23 ga watan Mayu domin buga karawar karshe ta mako na 38 a gasar ta Premier League ta bana.

Haka kuma United za ta buga wasan karshe a Europa League tsakaninta da Villareal ranar 26 ga watan na Mayu.

Sau daya United ta karkare kakar Premier a mataki na biyu a teburi tun bayan da Sri Alex Ferguson ya yi ritaya a 2013.