Atletico ta lashe kofin La Liga na bana a ranar karshe

Luis Suarez

Asalin hoton, Getty Images

Atletco Madrid ta yi nasarar daukar kofin La Liga na bana, bayan da ta doke Real Valladolid da ci 2-1 a wasan mako na 38 na karshe a kakar 2020/21 a Spaniya.

Valladolid ce ta fara cin kwallo a minti na 18 da fara tamaula ta hannun Oscar Plano, kuma haka suka je hutu da wannan sakamakon.

Bayan da suka yi hutu suka koma karawa ta biyu ce, Atletico ta farke ta hannun Angel Correa daga nan Luis Suarez ya ci mata na biyu.

Da wannan sakamakon Atletico ta zama ta daya a babbar gasar Spaniya ta bana da maki 86, yayin da Real Madrid wadda ta ci Villareal 2-1 ta hada maki 84 a mataki na biyu.

Barcelona wadda ta je ta doke Eibar da ci 1-0 ranar Asabar ta karkare kakar bana a mataki na uku da maki 79, yayin da Sevilla mai maki 74 ta yi ta hudu a kakar 2020/21.

Real Madrid ta kare kakar bana ba tare da cin kofi ba, ita kuwa Barcelona ta tsira a Copa del Rey na shekarar nan.

Real Valladolid wadda ta sha kashi a hannun Atletico da ci 2-1 ta kammala wasannin bana a mataki na 19 da maki 31 za ta koma buga karamara gasa a badi kenan.

Sauran biyun da za su bar La Liga zuwa karamar gasa sun hada da Huesca mai maki 34 ta 18 a kasan teburi da kuma Eibar ta karshe ta 20 wadda ta karkare da maki 30.

Wannan shi ne kofin La Liga na farko da Atletico ta lashe tun bayan kakar 2013/14, kuma na 11 jumulla kenan a gasar ta Spaniya.

Real Madrid ce ta daya a yawan lashe La Liga a tarihi mai 34, sai Barcelona ta biyu da take da 26, sannan Atletico ta uku mai 11, inda Athletic Bilbao take da takwas a tarihi.

Sakamakon wasannin mako na 38 da aka buga ranar Asabar:

  • Celta Vigo 2-3 Real Betis
  • Osasuna0-1 Real Sociedad
  • Real Madrid 2-1 Villarreal
  • Real Valladolid 1-0 Atletico Madrid
  • Eibar 0-1 Barcelona
  • Elche 2-0 Athletic Bilbao
  • Huesca 0-0 Valencia

Wasa biyu da za a karkare ranar Lahadi 23 ga watan Mayu:

  • Granada da Getafe
  • Sevilla da Deportivo Alaves