Lionel Messi ya lashe takalmin zinare a La Liga ta bana

Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

Barcelona ta tsira da Copa del Rey a kakar 2020/21, bayan da Atletico Madrid ta dauki La Liga a karon farko tun bayan 2013/14.

Shi kuwa Lionel Messi shi ne ya lashe takalmin zinare a matakin wanda ke gaba a cin kwallaye a gasar ta Sifaniya ta kakar nan.

Messi ya zura kwallo 30 a raga a bana ya kuma karbi kyautar da ake kira ta Pichichi, kuma karo na biyar a jere yana bajintar karo na takwas jumulla a tarihi.

Takalmin zinare takwas da ya lashe a La Liga a tarihi:

  • Kakar 2009/10 (kwallo 34)
  • Kakar 2011/12 (kwallo 50)
  • Kakar 2012/13 (kwallo 46)
  • Kakar 2016/17 (kwalo 37)
  • Kakar 2017/18 (kwallo 34)
  • Kakar 2018/19 (kwallo 36)
  • Kakar 2019/20 (kwallo 25)
  • Kakar 2020/21 (kwallo 30)

Kawo yanzu Messi ne kan gaba a matakin wanda ya lashe takalmin zinare da yawa a gasar La Liga, kuma shi ne ke rike da bajintar cin biyar a jere.

A gasar ta La Liga wanda ya yi nasarar lashe kyautar ta Pichichi shi ne Telmo Zarra mai guda shida.

Haka kuma Hugo Sanchez da Alfredo Stefano sun ci biyar-biyar kowanne a La Liga, kuma hur hudu suka lashe a jere a lokacin da suka taka leda a tarihi.

Wadanda suke da tarihin lashe takalmin zinare da yawa a gasar kulob din Turai:

A Jamus, Gerd Muller ya lashe lambar yabo ta yawan cin kwallaye a gasar Bundesliga har karo biyar a tarihi.

A gasar Italiya ta Serie A kuwa, Gunnar Nordahl ya lashe takalmin zinare biyar a karni na 1950 a AC Milan.

A Faransa, Jean-Pierre Papin ya karbi kyautar cin kwallaye karo biyar a lokacin da ya taka leda a Marseille.

Tsohon dan wasan Arsenal, Thierry Henry ya kalbi takalmin zinare hudu a Premier League, shi kuwa Ruud Geels ya yi bajinta karo biyar a lokacin da ya taka leda a Ajax da kuma Sparta Rotterdam.

Kawo yanzu yarjejeniyar Messi a Barcelona za ta kare a karshen kakar bana wato ranar 30 ga watan Yuni.

Shin ko Messi zai tsawaita zamansa a Sifaniya ko kuma zai bar Barcelona ne?