Kano Pillars ta sake dare teburin Firimiyar Najeriya

Nigerian Premier League

Asalin hoton, Npfl

Kano Pillars ta yi nasarar doke Nasarawa United da ci 1-0 a wasan mako na 23 da suka fafata a gasar cin kofin Firimiyar Najeriya ranar Laraba.

Pillars ta ci kwallon ta hannun Auwalu Ali Mallam a minti na 25 da fara tamaula, kawo yanzu dan wasan ya ci kwallo hudu ya kuma bayar da shida aka zura a raga.

Da wannan sakamakon Pillars ta hada maki 44, bayan buga karawar mako na 23, Akwa United wadda ta yi wasa 22 ta koma ta biyu da maki 41.

Sakamakon wasannin mako na 23 da aka kara ranar Laraba:

  • Kwara United 1-1 Rivers United
  • Dakkada 2-1 FC Ifeanyiubah
  • Warri Wolves 1-0 Lobi Stars
  • Adamawa United 1-0 Katsina United
  • Wikki Tourist 1-2 Enyimba Internatiolal
  • Sunshine Stars 0-0 Mountain of Fire and Miracle

Ranar 27 ga watan Mayu za a yi wasa biyu:

  • Enugu Rangers International da Jigawa Golden Stars
  • Abia Warriors da Akwa United

An kuma dage karawa tsakanin Heartland da Plateau United da ya kamata a fafata ranar Laraba.