Zidane ya ajiye aikin horas da Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images
Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya ajiye aikinsa na horas da kungiyar a karo na biyu.
Real ta gaza cin ko wane irin kofi a wannan kakar ta bana, a La Liga kuma abokiyar hamayyarta da gari daya Atletico Madrid a ranar Asabar din da ta gabata.
Zidane mai shekara 48, ya lashe Champions sau uku a jere a lokaci na farko da yake tafiyar da kungiyar tsakanin shekarar 2016 da 2018.
Ya kuma koma kungiyar inda ya yi watanni 10 kuma ya kammala gasar La Liga a matsayi na biyu.
Tun shekarar 2009-10 rabon da ace Real ta gaza cin kofi ko daya a tarihi.
Tun da wuri aka cire ta daga gasar Copa del Rey, kuma wata kungiya ce da ke buga matsayi na uku a Sifaniya Alcoyano ce ta cire ta.
A kuma gasar zakarun Turai kuma Chelsea ce ta cire Real a matakin wasan daf da na karshe.
"Zidane na daya daga cikin manyan 'yan wasan Real Madrid da suka cimma tarihi a kungiyar, kuma ya kara fadada nasarorinsa a kungiyar lokacin da ya zama kocin kungiyar" a sanarwar da kungiyar ta fitar.
" Ya san cewa yana cikin zuciyoyin magoya bayan Real Madrid kuma ko da yaushe Real Madrid gida ce a wurin shi."
A farkon wannan watan ne Zidane ya musanta rahoton da ke cewa ya shaida wa 'yan wasansa cewa zai bar kungiyar a karshen wannan kakar.
Maganar zamansa a kungiyar ce ta mamaye jaridun Sifaniya, wanda suka ba da gudun mawar kawo sauye-sauye, kan cewa shi da 'yan wasansa na bukatar girmamawa ta musamman.
Shi ne kadai kocin da ya taba cin Champions sau uku a jere, cikin kuma kofinan da ya ci sun hada da: kofin kwararrun na duniya, da Super Cup biyu da kuma Super Cup na Sifaniya biyu.






