Thomas Tuchel ya lashe Champions League a karon farko

Chelsea Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Chelsea ta yi nasarar lashe Champions League na bana, bayan da ta doke Manchester City da ci 1-0 ranar Asabar a Porto, Portugal.

Kai Havertz ne ya ci kwallon da ya bai wa Chelsea kofin Zakarun Turai karo na biyu a tarihi.

Wannan shi ne karon farko da kocin Chelsea, Thomas Tuchel ya lashe Champions League a tarihin sana'ar horar da tamauala.

Ko a bara sai da ya kai Paris St Germain wasan karshe, amma Bayern Munich ta yi nasara da ci 1-0.

Cikin watan Janairu Paris St Germain ta sallami Tuchel, wanda Chelsea ta dauka ya kuma maye gurbin Frank Lampard a lokacin da kungiyar ta fita daga hudun farko.

Chelsea ta karkare kakar Premier ta bana a mataki na hudu duk da rashin nasara da ta yi a gidan Aston Villa a wasan karshe, yayin da Liverpool ce ta kammala a mataki na uku.

Wannan shi ne karon farko da City wadda ta lashe kofin Premier League ta kai wasan karshe a Champions League.

Pep Guardiola wanda yake da Champions League biyu da ya lashe a Barcelona ya fara karawar da Fernandinho da kuma Rodri a benci, inda ya jere masu cin kwallaye a gaba.

City ta samu damar makin zura kwallao a raga tun kan hutu, har da wadda Phil Foden ya buga amma Antonio Rudiger ya hana kwallon shiga raga.

Wadanda suka buga wasan:

Manchester City: Ederson da Walker da Stones da Dias da Zinchenko da Gundogan da Bernardo Silva da De Bruyne da Mahrez da Foden da kuma Sterling

Wadanda suka shiga daga baya a City: Fernandinho da Gabriel Jesus da kuma Aguero.

Chelsea: Mendy da Azpilicueta da Thiago Silva da Rudiger da James da Chilwell da Kante da Jorginho da Mount da Havertz da kuma Werner

Wadanda suka shiga daga baya a Chelsea: Christensen da Kovacic da kuma Pulisic,.

An ci klwallo: Havertz a minti na 42.

Alkalin wasa: Mateu Lahoz Sifaniya.

Katin gargadi: Gundogan na Manchester City da Rudiger na Chelsea da Gabriel Jesus na Manchester City