'Yan Real Madrid dake buga tamaula a Olympic a Tokyo

Real Madrid Players in Tokyo Olympic

Asalin hoton, Real Madrid FC

'Yan wasan Real Madrid hudu ne ke buga gasar kwallon kafa a Olympic da za a yi bikin bude wasannin ranar 23 ga watan Yuni a birnin Tokyo.

Cikin 'yan kwallon sun hada da Asensio da Ceballos da kuma Vallejo masu wakiltar Sifaniya da Takefusa Kubo, wanda zai buga wa Japan tamaula.

Tuni aka fara gasar kwallon kafa ta maza da ta mata wadda ake yi tun kan bikin bude wasannin, an kuma tashi karawa tsakanin Masar da Sifaniya 0-0.

Sauran wasan da Sifaniya za ta buga shine da Australia ranar 25 ga watan Yuli, sannan ta karkare da wasan karshe a cikin rukuni da Argentina ranar 28 ga watan Yuli.

Japan kuwa wadda Takefusa Kubo ke wakilta ta yi nasara a kan Afirka ta Kudu da ci 1-0, kuma Kubo ne ya ci kwallon saura minti 19 su tashi daga fafatawar.

Ranar Lahadi 25 ga watan Yuli, Japan za ta buga wasa na biyu da Mexico, sannan ta karkare da Faransa ranar 28 ga watan Yuli a karawar cikin rukuni.

Brazil ce ke rike da lambar zinare, wadda ta yi nasara a 2016 da ta karbi bakuncin wasannin, bayan doke Jamus a wasan karshe a bugun fenariti.

Tun a 2020 ya kamata a yi wasannin bana, amma bullar cutar korona ta sa aka dage wasannin zuwa 2021.

Sakamakon wasannin da aka buga a gasar kwallon kafar maza a Olympic:

  • Egypt 0 - 0 Spain
  • Mexico 4 - 1 France
  • New Zealand 1 - 0 Jamhuriyar Korea
  • Ivory Coast 2 - 1 Saudi Arabia
  • Argentina 0 - 2Australia
  • Japan 1- 0 Afirka ta Kudu
  • Honduras 0 - 1 Romania
  • Brazil 4 - 2 Jamus