Demarai Gray: Everton ta dauki dan wasan Bayer Leverkusen

Demarai Gray

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Demarai Gray ya fara taka leda a Birmingham City

Everton ta kammala daukar dan kwallon Bayer Leverkusen, Demarai Gray kan yarjejeniyar kaka uku kan kudin da ake cewa ya kai fam miliyan 1.7.

Cikin kunshin yarjejeniyar sayen dan wasan mai shekara 25, zai iya kara kaka daya kan ukun farko da aka amince, idan ya taka rawar gani.

Gray shine na uku da sabon koci, Rafael Benitez ya dauka zuwansa Everton a bana, bayan Andros Townsend da mai tsaron raga Asmir Begovic.

Gray, wanda ya lashe Premier League a Leicester a shekarar 2016, yana tare da Everton yanzu haka, wadda tana Amurka domin buga Florida Cup.

Wanda aka haifa a Birmingham, ya bar Leicester a Janairun 2021, wanda ya saka hannu kan yarjejeniyar wata 18 da Bayer Leverkusen, wadda ya yi wa kungiyar Jamus wasa 12 da cin kwallo daya a kakar da aka kammala.

Watakila dan kwallon Brazil da ke wasa a Everton, Bernard ya bar kungiyar, bayan da Sharjah ta Hadaddiyar Daulal Larabawa ke son zawarcinsa, wata kungiya a Rasha da Girka ma na son daukar dan kwallon.

Everton za ta buga Florida Cup a Amurka ba tare da Fabian Delph ba, bayan da ya killace kansa.

Dan wasan mai shekara 31 ya yi hulda da wani mutum da ya kamu da cutar korona, shi yasa kungiyar ta bukaci ya killace kansa.