Manchester City: Ba za ta buga wasan sada zumunta a Faransa ba

Manchester City boss Pep Guardiola watches on as Riyad Mahrez trains during pre-season

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Manchester City da Troyes suna rukunin kwallon kafar City ne

Manchester City ta soke wasan sada zumunta da Troyes, saboda dokar gwamnatin Burtaniya kan killace kai idan aka je Faransa.

Sabuwar dokar hana yada cutar korona a Burtaniya ta tanadi duk wanda zai koma Burtaniya daga Faransa, zai killace kai kwana 10, wanda hakan zai shafi shirin kungiyar Etihad don tunkarar kakar da za a fara cikin wayan Agusta.

Tun farko an tsara kungiyoyin biyun za su yi wasan sada zumunta ranar 31 ga wata Yuli a Faransa.

Wannan labarin ya zo ne, bayan da City ta sanar cewar za ta yi wasan sada zumunta da Preston ranar 27 - wanda za ta buga ba 'yan kallo.

City ta ce za ta buga karawar ba 'yan kallo a filin makarantar koyon tamaular kungiyar, bayan da aka rufe cibiyar tun 16 ga watan Yuli, bayan da aka samu wasu sun kamu da cutar korona.

Wasan da City za ta yi da Preston shine na farko tun bayan fafatawar karshe da Chelsea a Champions League ranar 29 ga watan Mayu.

City za ta bude kakar bana da Community Shield da Leicester City a Wembley ranar 7 ga watan Agusta, sannan ta fara wasan Premier da Tottenham ranar 15 ga watan Agusta.