Emile Smith Rowe: Dan wasan Arsenal ya sabunta yarjejeniya

Smith Rowe will wear the number 10 shirt for Arsenal in the upcoming season

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Smith Rowe zai sa riga mai lamba 10 a Arsenal daga kakar da za a fara cikin watan Agusta

Dan wasan Arsenal, Emile Smith Rowe ya saka hannu kan doguwar yarjejeniya da kungiyar.

Mai shekara 20, wanda ya fara Gunners tun daga matasan kungiyar, Aston Villa ta taya shi karo biyu, amma ba a sallama mata ba.

Smith Rowe ya fara yi wa Arsenal gasar Premier League a kakar 2020-21, wanda ya ci kwallo biyu ya kuma bayar da hudu aka zura a raga a kakar da ta wuce.

An bai wa Smith Rowe riga mai lamba 10 da zai saka a kakar 2021-22, wadda Dennis Bergkamp da kuma Mesut Ozil suka yi amfani da ita a kungiyar a baya.

Aston Villa ta taya shi fam milian 25 da fam miliyan 30 ga dan kwallon tawagar Ingila ta matasa 'yan kasa da shekara 21,wanda saura kwantiragin kaka biyu ya rage kafin yanzu da ya kara kulla wata mai tsawo.

Arteta bai da niyyar sayar da dan kwallon wanda ya taka rawar gani a wasannin aro da ya yi a RB Leipzig da kuma Huddersfield Town.