Bernard na Everton ya koma Sharjar ta UAE

Bernard

Asalin hoton, Getty Images

Dan kwallon Brazil, Bernanrd ya bar Everton ya koma taka leda a Sharjah ta hadaddiyar Daulal Larabawa.

Sharjah ta sanar da daukar dan wasan mai shekara 28 a kafarta ta sada zumunta da cewa ya amince da kunshin yarjejeniyar kaka biyu.

Tsohon dan kwallon tawagar Brazil, ya bar Everton, wadda ya yi wa wasa 12 a Premier League a kakar da ta wuce karkashin Carlo Ancelotti.

Bernard ya yi karawa 73 a kaka uku da ya taka leda a kungiyar ta Goodison Park.

Ancelotti ya bar aikin kocin Everton zuwa Real Madrid cikin watan Yuni, tuni kungiyar ta maye gurbinsa da Rafael Benitez.