Paulinho ya koma Al Ahli ta Saudi Arabia

Paulinho

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Paulinho ya buga kaka biyu a Premier League a Tottenham

Tsohon dan kwallon Brazil, Paulinho ya saka hannu kan kwantiragin kaka uku da kungiyar Saudi Arabia, Al Ahli kamar yadda ta sanar ranar Juma'a.

Mai shekara 32 ya koma Al Ahli a matakin wanda bai da yarjejeniya, bayan da kungiyar China, Guangzhou FC ta amince ya koma buga wata gasar.

Paulinho ya taimakawa Guangzhou ta lashe Champions League na Asia a 2015, bayan da ya koma China da taka leda daga Tottenham.

Dan wasan ya taka leda a Barcelona a 2017 daga nan ya sake komawa Guangzhou a kakar 2018 ya kuma lashe gasar kwallon kafar China ta uku a 2019.

Paulinho shine na baya bayan nan da ya bar buga gasar China, sakamakon dokar kasar ta hana yada cutar korona ga wadanda suke daga waje za su shiga kasar.

Abokin taka ledarsa a Guangzhou, Anderson Talisca ya koma kungiyar Saudi Arabia ta Al Nass a watan jiya, shi kuwa Renato Augusto, wanda ya taka leda a Beijing Guoan, yanzu yana Corinthians ta Brazil.