Bale da Kroos da Varane sun koma atisaye a Real

Gareth Bale

Asalin hoton, Getty Images

Greath Bale yana daga cikin 'yan Real Madrid uku da suka koma Sifaniya don karbar horon tunkakar kakar da za a fara cikin watan Agusta wato gasar 2021-22..

Bale mai shekara 32, wanda bai da makoma a Real ya buga wasannin aro a kakar da ta wuce a Tottenham, wanda ya kasa taka rawar da ta kamata don nuna kansa ko ya koma buga Premier League.

Yanzu dai Bale ya koma Real Madrid don ci gaba da wasa karkashin koci Carlo Ancelotti, wanda suka yi aiki tare kaka biyu a farkon horar da kungiyar da dan kasar Italiya da ya yi.

Sauran da suka koma karbar horo a Real bayan Bale sun hada da Toni Kroos da kuma Raphael Varane, wanda ake cewar ba zai ci gaba da taka leda a kungiyar ba, bayan da Ramos ya koma Paris St Germain.

Sauran kwantiragin kaka daya ya ragewa Varane a Real Madrid, ana kuma cewar Manchester United tana tattaunawa da kungiyar Sifaniya don daukar mai tsaron bayan tawagar Faransa.

Karim Benzema ya kamata ya fara atisaye ranar Juma'a, sai dai ya ci karo da koma baya, sakamakon kamuwa da cutar korona da ya yi.