Blessing Okagbare: An dakatar da 'yar tseren Najeriya daga gasar Olympics 2020

Blessing Okagbare

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Okagbare ta lshe tseren mita 100 a ranar Juma'a kafin dakatawar

Hukumar gasar Olympics da ke gudana a Japan ta dakatar da 'yar tseren Najeriya, Blessing Okagbare, daga gasar saboda ba ta tsallake gwajin shan ƙwayoyi masu ƙara kuzari ba.

A ranar Juma'a ne Okagbare mai shekara 32 wadda ta ƙware a tsere da kuma tsalle, ta lashe tseren mita 100 sannan ta samu gurbin shiga zagayen kusa da na ƙarshe da za a yi ranar Asabar.

Sashen kula da halayen 'yan wasa na Athletics Integrity Unit (AIU) ya ce an gano 'yar tseren ta sha ƙwayar da ke ƙara wa wasu ƙwayoyin halittar ɗan Adam ƙarfi biyo bayan wani gwaji da aka yi mata tun ranar 19 ga watan Yuli.

AIU ya ce an sanar da Okagbare game da dakatarwar a ranar Asabar.

'Yar wasan wadda ta lashe kyautar azurfa (silver) a birnin Beijing a 2008, ta yi nasara a tseren mita 100 cikin daƙiƙa 11.05, an tsara za ta kara da Asher-Smith da kuma 'yar Jamaica mai suna Elaine Thompson-Herath a wasan kusa da na ƙarshe.

Dakatarwar tata na zuwa ne kwana biyu bayan an hana 'yan wasan Najeriya 10 shiga gasar bisa dalilin rashin cancanta.

AIU ya ce ba za su shiga gasar ba saboda sun ƙi shiga a yi musu gwajin ƙwayoyin ƙara kuzari da ake yi kafin fara gasar ta Olympics.