Crystal Palace: Gary Cahill ya bar Crystal Palace

Gary Cahill

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Gary Cahill ya buga wa tawagar Ingila wasa 61

Gary Cahill ya bar Crystal Palace, bayan da yarjejeniyarsa ta kare da kungiyar mai buga gasar Premier League.

Mai shekara 35, mai tsaron baya ya koma Selhurst Park da taka leda kan kwantiragin kaka biyu a Agustan 2019, bayan da ya bar Chelsea.

Sabon kocin Palace, Patrick Vieira ya dauki masu tsaron baya a bana da suka hada da Joachim Andersen da kuma Marc Guehi.

Cahill ya lashe Premier League da FA Cup da League Cup da Champions League da Europa League a lokacin da ya taka leda a Chelsea.

Tsohon dan kwallon Bolton da Aston Villa ya yi wa tawagar Ingila wasa 61, daga baya ya yi ritayar buga mata tamaula bayan kammala gasar kofin duniya ta 2018.