Barcelona za ta gabatar da Emerson ran Litinin

Emerson Royal

Asalin hoton, Getty Images

Ranar Litinin Barcelona za ta gabatar da Emerson Royal a matsayin sabon dan wasanta a Camp Nou.

Tun a makon jiya dan kwallon tawagar Brazil ya je Barcelona domin shirin gabatar da shi ga mahukuntan kungiyar da kuma ganawa da 'yan jarida.

Ranar 2 ga watan Yunin 2021, Barcelona ta kammala cinikin dan wasan na Atletico Mineiro da Real Betis.

Mai tsaron bayan Brazil ya yi hutu ne, bayanm kammala gasar Copa America, wanda ya wakilci kasarsa a gasar da ta karbi bakunci.

Ranar 31 ga watan Janairun 2019, Barcelona ta cimma yarjejeniyar daukar dan wasan tsakanin Atletico Mineiro da Real Betis, wadda ya yi wa wasannin aro, sannan ta saye shi.

Mai shekara 22, wanda aka haifa a Sao Paulo ya fara taka leda a matakin kwararren dan wasa a Ponte Preta daga 2016 zuwa 2018.

Ya koma Atletico Mineiro a 2018, wadda ta bayar da shi aro ga Real Betis a 2019, sannan ta mallaki dan kwallon daga baya.

A kakar da ta wuce shine kan gaba a buga wa Manuel Pellegrini wasanni a La Liga a Real Betis, wanda ya ci kwallo biyar ya kuma bayar da 10 aka zura a raga.