Andriy Shevchenko: Tsohon dan wasan Chelsea ya bar aikin horar da Ukraine

Andriy Shevchenko

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Andriy Shevchenko ya kai Ukraine quarter final a European Championship a karon farko a tarihin kasar

Andriy Shevchenko ya ajiye aikin horar da tawagar Ukraine, kamar yadda ya sanar a kafar sada zumuntarsa ta Instagram.

An nada Shevchenko, mai shekara 44, aikin jan ragamar Ukraine a 2016 ya kuma kai kasar karawar quarter-finals a Euro 2020, wadanda Ingila ta yi waje da su da 4-0 a Rum.

Shevchenko, wanda ya yi ritayar buga wa Ukraine tamaula a 2012, shine kan gaba a ci wa kasar kwallaye mai 48 a fafatawa 111.

Ya fara taka leda a Dynamo Kyiv daga nan ya koma AC Milan a 1999, inda ya ci manyan kofi biyar har da Serie A da Champions League, sannan ya lashe kyautar Ballon d'Or a 2004.

Shevchenko ya koma wasa a Chelsea a 2006 kan fam miliyan 30, inda ya ci FA Cup da League Cup, sannan ya koma Milan buga karawar aro a 2008.

Daga baya ya bar Stamford Bridge ya sake komawa Dynamo Kyiv, wadda ya fara tun a matashin dan kwallo..