Jose Mourinho: An kori kocin Roma a wasan sada zumunta da Real Betis ta ci 5-2

Jose Mourinho is sent off during Roma's friendly with Real Betis

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Cikin watan Mayu aka nada Jose Mourinho sabon kocin Roma

An kori kocin Roma, Jose Mourinho a wasan sada zumunta da Real Betis ta yi nasara da ci 5-2 ranar Asabar.

Mai masaukin baki Betis ta ci 3-2 a minti na 57, inda ta ukun 'yan wasan Roma, ke kalubalantar Alex Moreno cewar kwallon da ya ci ya sa hannu.

Ana tsaka da wasa Lorenzo Pellegrini ya yi laifin da ya karbi kati mai ruwan dorawa na biyu, da jankati aka kuma kori Mourinho daga fili, bayan korafin da ya yi kan sallamar masa dan kwallo.

An kuma bai wa Gianluca Mancini da Rick Karsdorp kowanne katin gargadi na biyu da kuma jan kati da ta kai Betis ta kara cin kwallo biyu da suka tashi 5-2 a fafatawar da suka yi a Seville.

Real Betis za ta fara buga wasan farko a gasar La Liga da ziyartar Real Mallorca ranar Asabar 14 ga watan Agusta.

A kuma ranar Roma za ta buga wani wasan sada zumunta da Raja Casablanca ta Morocco, sannan ta kara a wasan neman gurbin shiga Europa Conference League ranar 19 ga watan Agusta.

Roma za ta fara karawar farko a gasar Serie A ta bana a gidan Fiorentina ranar 22 ga watan Agusta.

Inter Milan ce ta lashe Serie A na kakar da aka karkare, kofin farko na babbar gasar Italiya da ta lashe tun bayan 2010.