Barcelona ta lashe kofin Joan Gamper, bayan doke Juventus 3-0 a wasan da suka yi a Johan Cruyff

Barcelona FC

Asalin hoton, Getty Images

Barcelona ta doke Juventus da ci 3-0 ta ci kofin Joan Gamper a karawar da suka yi ranar Lahadi a filin wasa na Johan Cruyff.

Kungiyar ta Sifaniya ta ci kwallayen ta hannun Memphis Depay minti na uku da fara wasa, sai Martin Braithwaite ya ci na biyu, bayan da suka koma karawa ta biyu.

Barcelona wadda ta buga wasan ba tare da Lionel Messi ba a karon farko tun bayan shekara 21 ta ci kwallo na uku ta hannun Riqui Puig daf da za a tashi daga karawar.

Ranar 15 ga watan Agusta Barcelona za ta fara wasan farko a gasar La Liga ta 2021-22, inda za ta karbi bakuncin Real Sociedad a Camp Nou.

'Yan kwallon Barcelona da suka kara da Juventus a Camp Nou:

'Yan wasan sun hada da Dest da Pique da R. Araujo da Sergio da Riqui Puig da Griezmann da Pjanic da Memphis da Braithwaite da Neto da kuma Coutinho.

Sauran sun hada da Jordi Alba da S. Roberto da E. Royal da Umtiti da Inaki Pena da Demir da Nico da R. Manaj da Balde da kuma Collado.

Philippe Coutinho ya murmure yana daga cikin ';yan wasan da aka bayyana, yayin da Clement Lenglet da kuma Sergio Aguero ke jinya.

'Yan wasan Juventus da suka ziyarci Barcelona:

 • Wojciech Szczesny
 • Mattia Perin
 • Carlo Pinsoglio
 • Mattia De Sciglio
 • Giorgio Chiellini
 • Matthijs de Ligt
 • Danilo Luiz
 • Juan Cuadrado
 • Alex Sandro
 • Luca Pellegrini
 • Leonardo Bonucci
 • Daniele Rugani
 • Koni De Winter
 • Aaron Ramsey
 • Weston McKennie
 • Federico Bernardeschi
 • Federico Chiesa
 • Rodrigo Bentancur
 • Filippo Ranocchia
 • Cristiano Ronaldo
 • Alvaro Morata
 • Dejan Kulusevski
 • Alejandro Marques