Barca ta yi wasa karon farko ba Messi tun bayan shekara 21

Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

Barcelona ta yi nasara a kan Juventus da ci 3-0 ta lashe kofin Joan Gamper da suka kara a Johan Cruyff ranar Lahadi.

Barcelona ta karbi bakuncin Juventus tare da Cristiano Ronaldo ba tare da Messi ba a karon farko tun bayan shekara 21 da ya yi a kungiyar.

Kyaftin din tawagar Argentina ya yi shekara 21 a Barcelona da karawa kaka 17 da ya buga wa babbar kungiyar tamauala, bayan lashe manyan kofuna da kyaututtuka a kungiyar.

Karon farko da kungiyar ta yi wasa ba tare da Messi ba a matakin dan kwallonta, mai saka riga lamba goma da wasu ke kiraye-kirayen a rataye rigar har abada a Barcelona.

Kocin Barcelona ya fayyace wadanda suka buga mata wasan haka itama Juventus ta fadi wadanda ta je da su Sifaniya

Messi ya fara buga tamaula tun yana dan karami a Grandoli tsakanin 1992 zuwa 1995 daga nan ya koma Newell Old Boys daga 1995 zuwa 2000.

Ya koma Barcelona daga 2000, wanda ya fara wasa a karamar kungiyar ta biyu daga 2003 zuwa 2004, ya kuma kai matakin karamar kungiyar ta farko a 2004 zuwa 2005.

Daga nan ya fara taka leda a babbar kungiyar tsakanin 2004 zuwa kakar bana ta 2021.

Ga jerin kofunan da ya lashe a Barcelona:

La Liga: 2004-05, 2005-06, 2008-09, 2009-10, 2010-11, 2012-13, 2014-15, 2015-16, 2017-18, 2018-19

Copa del Rey: 2008-09, 2011-12, 2014-15, 2015-16, 2016-17, 2017-18, 2020-21

Supercopa de España: 2006, 2009, 2010, 2011, 2013, 2016, 2018

UEFA Champions League: 2005-06, 2008-09, 2010-11, 2014-15

UEFA Super Cup: 2009, 2011, 2015

FIFA Club World Cup: 2009, 2011, 2015