Lautaro Martinez: Tottenham na kokarin sayen dan kwallon Inter Milan mai cin kwallaye

Lautaro Martinez

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Atisayen da Martinez ke yi kenan kafin fara gasar Serie A ta bana da za a fara ranar 21 ga watan Agusta

Tottenham na ta kokarin sayen dan wasan Inter Milan mai cin kwallaye, Lautaro Martinez, wanda ake cewar kudin daukarsa zai kai fam miliyan 60.

Martinez, mai shekara 23 ya ci kwallo 49 a wasa 132 da ya buga wa Inter, tun bayan da ya koma kungiyar daga Racing Club ta Argentina a 2018.

Dan wasan yana daga wadanda suka taka rawar da Inter Milan ta lashe Serie A a kakar da ta wuce, kofin farko tun bayan 2010.

Yana cikin 'yan wasan da suka bayar da gudunmuwa da tawagar Argentina ta lashe Copa America a watan jiya a Brazil.

Tottenham ta kashe kudi fiye da fam miliyan 60 daga ranar Juma'a, bayan cinikin da ta sayi mai tsaron baya Cristian Romero daga Atalanta kan fam miliyan 42.5.

Ta kuma dauki dan wasa Bryan Gil daga Sevilla a watan Yuli da kuma karbar aron Pierluigi Gollini daga Atalanta.

Inter Milan ta ci karo da matsin tattalin arzikin da cutar korona ta haddasa, bayan da uwar kungiyar Suning ke fama da matsalar karacin kudi.

Idan har Tottenham ta dauki Martinez, zai bude kofar cewar Harry Kane zai je Manchester City kenan da taka leda a bana.

Kane bai buga wa Tottenham wasan sada zumunta da Arsenal ba, wanda ya killace kansa ke yin atisaye shi kadai, bayan da ya kammala hutun buga Euro 2020.

Ranar Juma'a Kane ya sanar cewar bai kauracewa wajen atisaye ba, bayan da bai koma kungiyar daga hutu kan lokaci ba.

Kocin Manchester City, Pep Guardiola ya tabbatar cewar suna da sha'awar daukar Kane dan kwallon tawagar Ingila.