Joe Willock: Newcastle ta amince za ta dauki dan wasan Arsenal kan sama da fam miliyan 20

Joe Willock

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Willock ya ci wa Newcastle kwallo bakwai a wasa bakwai a karshe-karshen kammala Premier League da aka kammala

Newcastle United ta cimma yarjejeniya da Arsenal kan za ta sayi Joe Willock kan kudi sama da fam miliyan 20.

Kocin Newcastle, Steve Bruce bai boye aniyar mallakar dan wasan mai shekara 21 ba, wanda ya taka rawar gani a wasannin aro da ya yi wa kungiyar a kakar da aka kammala.

Willock ya ci kwallo bakawi a jere a wasa bakwai a gasar Premier League da suka taimakawa kungiyar ta ci gaba da zama a babbar gasar tamaula a Ingila, tun bayan da ya je kungiyar a watan Janairu.

Kocin Arsenal, Mikel Arteta bai amsa tambayar da 'yan jarida suka yi masa ba kan dalilin da ba a ga Willock a wasan da Gunners ta yi rashin nasara a hannun Tottenham ba ranar Lahadi.

Dan kwallon tawagar Ingila ta matasa 'yan kasa da shekara 21, ya buga wa Arsenal wasa bakwai a Premier League a kakar da ta wuce.

Ana alakanta Arsenal da cewar za ta maye gurbin Willock da dan wasan Leicester City, James Maddison, sai dai Brendan Rodgers ya ce dan wasan bana sayarwa bane.