Sergio Aguero: Dan wasan Barcelona zai yi jinyar mako 10

Sergio Aguero

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sergio Aguero ya koma Barcelona daga Manchester City cikin watan Yuni

Kungiyar Barcelona ta sanar da cewar Sergio Aguero zai yi jinyar mako 10, ba za a fara gasar La Liga ta bana da shi ba.

Kungiyar ta fitar da wani bayani da ya tabbatar da raunin dan kwallon tawagar Argentina.

Aguero, mai shekara 33, ya koma Barcelona daga Manchester City kan yarjejeniyar kaka biyu, bayan da yarjejeniyarsa ta kare a Etihad.

Dan kwallon wanda ya yi kaka 10 a City, ya zama kan gaba a ci wa kungiyar kwallaye mai 260 a raga a fafatawa 390.

Aguero ya lashe Copa America a watan jiya a tawagar Argentina tare da Lionel Messi wanda ya tabbatar da barin Barcelona.