Bojan Krkic: Tson dan wasan Barcelona da Roma ya koma buga gasar Japan

Bojan Krkic

Asalin hoton, Getty Images

Tsohon dan kwallon Barcelona da Roma, Bojan Krkic ya koma kungiyar Vissel Kobe mai buga gasar tamaula ta Japan.

Mai shekara 30 tsohon dan kwallon Barcelona zai taka leda tare da Andres Iniesta, wadanda suka buga tamaula a Camp Nou daga 2007 zuwa 2011.

Bojan ya koma Japan da taka leda bayan buga gasar Amurka tare da Montreal Impact, bayan da Kobe ke fatan taka rawar gani a wasannin bana.

Dan kwallon ya buga wa aAjax wasannin aro, sai ya koma Stoke City daga nan ya je Alaves wasannin aro, sai Montreal Impact ta dauke shi.

Zuwansa Kobe ya kara yawan 'tsoffin 'yan kwallon Barcelona a kungiyar wadda kamfanin Rukuten ya mallaka da Barcelona ke yi wa tallace-tallace a riga.

Bayan Iniesta da Bojan da suka murza leda a Camp Nou da akwai Sergi Samper da kuma Thomas Vermaelen da suke kungiyar ta Japan.

Shi kuwa David Villa ya buga wa Kobe wasanni a baya can.