Barcelona ta nada sabon kyaftin magajin Messi

Barcelona Captain

Asalin hoton, Getty Images

Bayan da Lionel Messi ya bar Barcelona, kungiyar ta sanar da 'yan wasa hudu da za su ke yi mata kyaftin.

Sergio Busquets shine magajin Messi a matakin kyaftin din kungiyar, sai Gerard Pique mataimakin sannan Sergio Roberto da kuma Jordi Alba.

Busquets da Pique da kuma Sergi Roberto sun yi mataimakan Messi a baya a kungiyar, yanzu kuma Barcelona ta kara da sunan Jordi Alba.

Mai tsaron baya Alba ya ja ragamar tawagar Sifaniya a Euro 2020, bayan da Busquet ya killace kansa, sakamakon kamuwa da cutar korona.

A wasan da Barcelona ta doke Juventus 3-0 ranar Lahadi ta lashe kofin Joan Gamper, Busquets ya fara daura kyallen kyaftin din kungiyar.

Dukkan 'yan wasan hudu sun fara Barcelona daga makarantar koyon tamaula ta kungiyar da ake kira La Mesia.

Ana sa ran Messi zai koma Paris St Germain da taka leda, bayan barin Barcelona, wadda ya yi kaka 21 a kungiyar.