Africa Cup of Nations: Algeria tana cikin rukuni na biyar

Africa Cup of Nations

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Algeria ta doke Senegal a wasan karshe a 2019 da ta lashe kofin nahiyar Afirka na biyu a tarihi

An raba jadawalin gasar cin kofin nahiyar Afirka ranar Talata a Kamaru, wanda aka yi bikin a Yaounde.

Mai rike da kofin Algeria, karkashin Djamel Belmadi, ta kafa tarihin buga wasa 27 a jere ba tare da yin rashin nasara ba.

Wannan kokarin ya sa masana na cewar Algeria za ta iya sake daukar kofin nahiyar Afirka da za a yi a Fabrairu kuma karo na uku a tarihi da za ta yi bajintar.

Cikin jadawalin da za aka raba na kasashe 24 ya hada da 10 daga ciki da ko dai sun dauki kofin sau daya ko fiye da haka.

Tawagar Comoros da Gambia za su fara buga gasar kofin Afirka a karon farko a wasannin da za a tsakanin 9 ga watan Janairu zuwa 6 ga watan Fabrairu a Kamaru.

Kamaru ce ya kamata ta karbi bakuncin gasar da Masar ta gudanar a 2019 da Algeria ta zama zakara, bayan da kasar ta kasa kammala shiri da wuri.

Tun a cikin 2021 ya kamata a buga gasar kofin Afirka a Kamaru, bayan da aka sake bata izinin karbar bakunci, amma bullar cutar korona ta sa aka dage wasannin zuwa 2022.

Jadawalin gasar cin kofin Afirka da za a yi a 2022 a Kamaru:

Rukunin farko: Cameroon, Burkina Faso, Ethiopia, Cape Verde

Rukuni na biyu: Senegal, Zimbabwe, Guinea, Malawi

Rukuni na uku: Morocco, Ghana, Comoros, Gabon

Rukuni na hudu: Nigeria, Egypt, Sudan, Guinea-Bissau

Rukuni na biyar: Algeria, Sierra Leone, Equatorial Guinea, Ivory Coast

Rukuni na shida: Tunisia, Mali, Mauritania, Gambia

Yadda aka ware tukanen da aka saka kungiyoyin tun kan raba jadawalin:

  • Tukunyar farko: Kamaru da Algeria da Senegal da Tunisia da Morocco da kuma Najeriya
  • Tukunya ta biyu: Masaer da Ghana da Ivory Coast da Mali da Burkina Faso da kuma Guinea
  • Tukunya ta uku: Cape Verde da Gabon da Mauritania da Sierra Leone da Zimbabwe da kuma Guinea-Bissau
  • Tukunya ta hudu: Malawi da Sudan da Equatorial Guinea da Comoros da Habasha da kuma Gambia