Lukaku ''na sake komawa'' Chelsea a matakin cikakken dan kwallo

Romelu Lukaku

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Cinikin 'yan wasa shida da aka yi mafi tsada a Birtaniya, Lukaku ya kafa tarihi daga biyu a ciki

Romelu Lukaku ya ce ya sake komawa Stamford Bridge a matakin kwararren dan wasa, tun bayan kaka biyu rabon sa da Premier League.

Mai shekara 28 ya koma Chelsea daga Inter Milan a makon jiya kan fam miliyan 97.5 a karo na biyu da zai buga mata tamaula, bayan zaman da ya yi tsakanin 2011 zuwa 2014.

"Yanzu ne nake cikakken dan kwallo. Na tanadi dukkan kwarewar da mai cin kwallaye ke bukata a wasanni, zan kuma kara kwazo a fannin da nake da rauni.'' in ji Lukaku.

Lukaku shine dan wasan da Chelsea ta saya mafi tsada a tarihi, kuma na biyu a tsada a Birtaniya, bayan Jack Grealish da Manchester City ta dauka daga Aston Villa a bana.

Dan wasan tawagar Belgium shine kan gaba a ci wa Inter kwallaye mai 24 a Serie A a kakar da ta wuce da kungiyar ta lashe kofin a karon farko tun bayan shekara 11.

Bayan da ya bar Stamford Bridge, Lukaku ya buga wasannin aro a Everton daga nan kungiyar ta saye shi, ya koma Manchester United a 2017.

Dan kwallon ya yi kaka biyu duk da magoya bayan United ba sa kaunar sa da cewar ya yi nauyi bai da kuzari.

Lukaku bai buga wa Chelsea karawar da ta doke Crystal Palace 3-0 ranar Asabar a wasan makon farko a gasar Premier.

Watakila ya fara yi wa Chelsea wasa a karawar da za ta yi da Arsenal ranar Lahadi.