Lionel Messi: Yaushe dan wasan Argentina zai fara buga wa PSG wasan farko?

Lionel Messi

Asalin hoton, PSG FC

Ranar Asabar Paris St Germain ta gabatar da Lionel Messi a gaban magoya bayanta, bayan da ya koma kungiyar daga Barcelona.

Messi ya koma Paris St Germain, bayan shekara 21 da ya yi a Camp Nou, bayan da Barcelona ta shiga matsin tattalin arziki.

Ranar Litinin shugaban Barcelona, Joan Laporta ya sanar cewar bashi ya yi wa kungiyar katutu da ya kai fam biliyan 1.35.

Matsin tattalin arzikin da Barcelona ta fada ne ya sa ta kasa tsawaita kwantiragin Messi, wanda ya amince da rage rabin albashin sa.

Tuni kyaftin din tawagar Argentina ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka biyu a PSG da sharadin za a iya tsawaitata kaka daya nan gaba.

Ranar Asabar PSG ta doke Strasbourg da ci 4-2 a wasan mako na biyu da fara gasar Ligue 1 ta bana.

Asalin hoton, Getty Images

Wadanda suka ci wa PSG kwallayen sun hada Mauro Icardi da Kylian Mbappe da Julian Draxler da kuma Pablo Sarabia.

Ita kuwa Strasbourg ta zare kwallo biyu ne ta hannun Kevin Gameiro da kuma Ludovic Ajorque.

Ranar Juma'a 20 ga watan Agusta, za a fara wasannin mako na uku a gasar Faransa da karawa tsakanin Stade Brest da Paris Saint-Germain.

Wasu na cewar da kyar ne idan Messi zai buga wasan ganin har yanzu bai koma kan ganiyar sa ba, bayan kammala Copa America da Argentina ta lashe a bana.

Haka kuma Paris St Germain za ta je Reims ranar 29 ga watan Agusta a karawar mako na hudu a Ligue 1 ta bana, watakila Messi ya buga fafatawar.

Mai shekara 34, wanda ya koma Faransa tare da iyalansa na neman wurin da zai samu kwanciyar hankali da zai mayar da hankali wajen taka leda.

Bayan wasannin gasar Faransa da ke gaban Messi zai kuma tunkari karawar neman shiga kofin duniya da Argentina za ta yi da Venezuela da Brazil da kuma Bolivia.