Africa Cup of Nations: Nageria tana rukuni na hudu a gasar kofin Afirka a Cameroon

Africa Cup of Nations

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Algeria ta doke Senegal a wasan karshe a 2019 da ta lashe kofin nahiyar Afirka na biyu a tarihi

Tawagar kwallon kafa ta Najeriya tana rukuni na hudu a gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a Kamaru a 2022.

A jadawalin da aka raba ranar Talara a Yahounde, Super Eales wadda ta ci kofin karo uku, tana rukunin da ya kunshi Masar da Sudan da kuma Guinea-Bissau.

Mai rike da kofin da ta lashe a 2019 a Masar, Algeria tana rukuni na biyar da ya hada da Sierra Leone da Ivory Coast da kuma Equatorial Guinea.

Mai masaukin baki, Kamaru tana rukunin farko da ya hada da Burkina Faso da Habasha da kuma Cape Verde.

Za a fara bikin bude gasar da karawa tsakanin Kamaru da Burkina Faso ranar 6 ga watan Janairu da ake sa ran karkare wasannin ranar 9 ga watan Fabrairun 2022.

Gasar da ta kunshi kasashe 24 za a fitar da gwanaye biyu a kowanne rukuni wato wadda ta yi ta daya da ta biyu kenan.

Za kuma a hada da tawagogi hudu da suka yi na uku-uku da maki mai kwari, domin kai wa zagaye na biyu a wasannin.

Tun a 2019 ya kamata Kamaru ta karbi bakuncin gasar kofin Afirka, amma ta kasa kammala shirin da ta kai aka bai wa Masar wasannin.

Hukumar kwallon kafar Afirka, Caf ta sake bai wa Kamaru izinin karbar bakuncin gasar 2021, amma cutar korona ta kai tsaikon da aka dage wasannin zuwa 2022.

Jadawalin gasar cin kofin Afirka da za a yi a 2022 a Kamaru:

Rukunin farko: Cameroon, Burkina Faso, Ethiopia, Cape Verde

Rukuni na biyu: Senegal, Zimbabwe, Guinea, Malawi

Rukuni na uku: Morocco, Ghana, Comoros, Gabon

Rukuni na hudu: Nigeria, Egypt, Sudan, Guinea-Bissau

Rukuni na biyar: Algeria, Sierra Leone, Equatorial Guinea, Ivory Coast

Rukuni na shida: Tunisia, Mali, Mauritania, Gambia