Pacos de Ferreira v Tottenham: Harry Kane ba zai buga Europa Conference League ba

Harry Kane

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Harry Kane bai buga wasa ba tun bayan da Italiya ta doke Ingila ta lashe Eueo 2020 a Wembley

Harry Kane ba zai buga wa Tottenham wasan neman gurbin shiga sabuwar gasar Conference League ba ranar Alhamis da za ta kara da Pacos de Ferreira.

Dan kwallon tawagar Ingila, wanda aka bayar da rahoton ya nemi barin Tottenham a bana, baya cikin 'yan wasan da kungiyar ta je da su Portugal ranar Laraba don karawar.

Kane mai shekara 28, bai buga wasan makon farko a gasar Premier League ba, wanda Tottenham ta yi nasara a kan Manchester City da ci 1-0.

Ya koma yin atisaye a kungiyar a kurarren lokaci, bayan hutun kammala gasar Euro 2020 da ya je ya yi a Amurka.

Tun farko an saka sunan Kane, cikin 'yan wasa 25 da za su fuskanci kungiyar Portugal, wadda ta yi ta biyar a teburi a kakar da ta wuce.

Duk wadda ta yi nasara a fafatawa biyun da za su yi gida da waje, za ta shiga sabuwar gasar nahiyar Turai ta uku, bayan Champions League da Europa League.

Kane na ta kokarin yin atisayen da zai koma kan ganiya, ana kuma sa ran zai buga wa Tottenham wasan Premier League da za ta buga da Wolves ranar Asabar.