Michy Batshuayi: Dan wasan Chelsea ya tsawaita zamansa, amma ya je Besiktas aro

Asalin hoton, Getty Images
Batshuayi ya ci kwallo takwas a wasa 33 da ya buga a kaka biyun da ya yi Crystal Palace
Michy Batshuayi ya koma Besiktas da zai mata wasannin aro, bayan da ya tsawaita yarjejeniya ci gaba da zama a Chelsea, wadda za ta kare a karshen kakar 2023.
Wannan shine karo na biyar da zai buga wasannin aro, tun bayan da ya koma Chelsea a 2016.
Tun farko Batshuayi ya je Borussia Dortmund da Valencia da kaka biyun da ya yi a Crystal Palace, wadda ya ci kwallo biyu a karawa 18 a kakar da ta wuce.
Rabonda dan kwallon tawagar Belgium yayiwa Chelsea wasa tun cikin watan Fabrairun 2020.
Kungiyar Turkiya, Besiktas, ita ce ta lashe gasar kasar a kakar 2020-21, za kuma ta buga Champions League a bana.
Tun bayan da dan wasan ya koma Stamford Bridge da taka leda daga Marseille kan fam miliyan 33, Batshuayi ya ci kwallo 25 a wasa 77 da ya yi Chelsea.
Ya zura kwallo shida a karkashin Frank Lampard a 2019-20, sai dai ya kasa samun buga wasanni da yawa, bayan da Tammy Abraham da Olivier Giroud na kan ganiya a lokacin.
Ya bayar da gudunmuwar da Chelsea ta ci Premier League a 2016-17, kakar da ya fara yi mata wasanni.
Chelsea ta sake daukar Romelu Lukaku a bana ta kuma sayar da Tammy Abraham ga Roma.