Antoine Griezmann: Dan kwallon Faransa ya yi wa Barcelona wasa 100

Antoine Griezmann

Asalin hoton, Barcelona FC

Antoine Griezmann ya buga wa Barcelona wasa 100, tun bayan da ya koma kungiyar daga Atletico Madrid a 2019.

Dan kwallon Faransa ya yi karawa ta 100 a wasan da Barca ta doke Real Sociedad 4-2 a wasan makon farko a La Liga ta bana ranar Lahadi.

Ranar Asabar din a Camp Nou, Barcelona ta buga La Liga a karon farko ba tare da Lionel Messi a matakin dan wasanta, wanda ya koma Paris St Germain da taka leda.

Gerard Pique ne ya fara ci wa Barca kwallo a minti na 19 da fara tamaula sannan Martin Braithwaite ya kara na biyu, minti biyu tsakani ya ci na uku na biyu da ya zura a raga.

A karawar Braithwaite ya zama dan kwallon Denmark da ya ci kwallo biyu a gasar ta La Liga a tarihi.

Saura minti takwas a tashi daga fafatawar Sociedad ta zare kwallo ta hannun Julen Lobete Cienfuegos, sannan minti uku tsakani Mikel Oyarzabal ya kara zare guda daya.

Tun bayan da tsohon dan kwallon Atletico ya koma Barcelona, kawo yanzu ya ci kwallo 35 a wasa 100 da ya ya yi wa kungiyar Camp Nou.

Saura kwallo 14 Griezman ya kamo tarihin yawan cin kwallaye da dan Faransa ya yi a kungiyar wato Thierry Henry mai 49, sai Ludovic Giuly na uku mai 26 a raga.

Bayan kwallo 35 da ya ci wa Barcelona ya kuma bayar da 16 aka zura a raga.

.