Cristiano Ronaldo: Juventus ta ce dan kwallon Portugal zai iya barin kungiyar

Cristiano Ronaldo in action for Juventus

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Cristiano Ronaldo ya ci kwallo 29 a wasan Serie A 33 a kakar da ta wuce

Juventus ta sanar da Cristiano Ronaldo cewar a shirye take ta sayar da shi da zarar ta samu tayi mai tsoka.

Kyaftin din tawagar kwallon kafar Portugal yana da sauran yarjejeniyar shekara daya a Juventus.

An dade ana ta rade-radin makomar sa a bana, wanda Juventus ba ta fara wasan makon farko da shi a Serie A ranar Lahadi ba a Udinese, amma ta saka shi daga baya.

Wakilin Ronaldo, Jorge Mendes ya tuntubi kungiyoyi a Turai da dama kan batun sayar da dan kwallon har da Manchester City da kuma Paris St-Germain.

Juventus ta zauna taro da Mendes ranar Alhamis tare da mahukuntan kungiyar ciki har da mataimakin shugaba Pavel Nedved da babban jami'i Maurizio Arrivabene da kuma daraktan wasannin Federico Cherubini.

Mendes ya ce da akwai yiwuwar tafiya ko zaman Ronaldo a Turin, sai dai Juventus ta ce ba za ta lamince dan kwallon ya bar kungiyar ba tare da an biya ta kudin da ta sayo shi kan fam miliyan 99.2 ba, shekara uku da ta wuce.

An fuskanci cewar Ronaldo baya farinciki da halin da ya tsinci kan sa, bayan da ya komawa Juventus daga Real Madrid.

Kungiyar ta kasa lashe Champions League dalilin da ta dauko dan kwallon Portugal kenan, inda Juventus ba ta taba haura quarter finals ba tun zuwa Ronaldo Turin, kuma sau biyu ana fitar da kungiyar a karawar zagaye na biyu a wasannin.

A kakar bara Juventus ta kasa cin kofin Serie A - bayan da lashe kofin karo tara a jere, wanda Inter Milan ta dauka, kuma a wasan karshe kungiyar Turin ta samu gurbin buga Champions League na bana.