Manchester City: Pep Guardiola ya ce zai bar Etihad da zarar kwantiragin sa ya kare a 2023

Asalin hoton, Getty Images
Pep Guardiola ya lashe kofin Premier League uku tare da Manchester City
Pep Guardiola ya ce zai bar Manchester City da zarar kwantiragin sa ya kare a 2023 a Etihad, daga nan yana fatan zai horar da wata kasar.
Mai shekara 50, wanda ya koma City cikin shekarar 2016 na shirin yin hutu da zarar kwantiragin sa ya kare, bayan jan ragamar kungiyar da ke buga Premier League.
"Ina jin ya kamata na dakata haka. Ina son na huta, sannan zan yi nazarin aikin da na gudanar,'' in ji Guardiola.
"Daga nan kuma aikin da zan yi gaba shine horar da tawagar kwallon kafar wata kasar.''
Ya kara da cewar ''Ina son horar da wata kasa a Kudancin Amurka don buga Copa America, Ina son jin yadda wasannin tamaula suke a nahiyar.''
Wannan labarin na Guardiola ya je kunnen mahukuntan kungiyar, bayan da Harry Kane ya ce zai ci gaba da taka leda a Tottenham a bana, maimakon buga tamaula a Etihad.
Guardiola wanda ya lashe Premier League uku da FA Cup da kuma League Cup hudu a jere a City, ya yi hutun wata 12, bayan da ya bar Barcelona a 2012 daga baya ya koma Bayern Munich.